Zanga-zangar yaki da cin hanci a majalisar dokokin Najeriya
October 6, 2016Kungiyoin matasan dai suna zaman dirshin ne cikin lumana ba tare da wata hatsaniya ko ihu ba a gaban majalisar dokokin Najeriyar a kan wannan batu na cin hanci a kasafin kudin na bana wanda tonon sililin da ya faru a tsakanin ‘yan majalisar ya sanya bankado shi da ya nuna sama da Naira bilyan 200 a ka cusa a cikin kasafin.Matasan da suka yi tataki daga wasu sassan kasar sun yi cincirundu a gaban majalisar dokokin Najeriyar suna masu cewar sai fa an dauki mataki a kan zargin kudadden da ‘yan majalisar ke rarrabawa kansu.Kwana na uku ke nan dai a jere suna zaman dirshin din na sai babba ta gani a kan wannan batu da ke kara daukan hankalin al'ummar Najeriyar.Tuni dai Hon Abdulmumini Jibril na majalisar da ya bankado zargin ya gabatar da bukatar binbcike ga hukumar EFCC abin da ya sanya dakatar da shi daga majalisar.Da alamun zargin aringizo a kasafin kudin wannan shekarar lamari da ake yi wa ‘yan majlaisar zai ci gaba da sanya tada jijiyar wuya da ma nuna 'yar yatsa a dai dai lokacin da ake ci gaba da jan dagga da ma ja in ja a kansa a Najeriyar, abin da tun farko ya haifar da jinkirin sanya shugaban Najeriya jinkirin sanya hannu a kasafin kudin.