Hadarin musayar wuta a Zaporizhzhya
August 25, 2022António Guterres ya kuma yi gargadi, kan mummunar illar da za a iya samu idan lamarin ya ta'azzara. Guterres ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya kara nuna damuwarsa kan halin da ake ciki a yankin tashar nukiliyar yana mai cewa kara tsananta musayar wuta a yankin yana da matukar hadari. Rasha dai ta kwace iko da tashar nukiliyar mafi girma a nahiyar Turai cikin watan Maris, kwanaki kalilan bayan ta kaddamar da yaki a makwabciyarta Ukraine. Musayar wuta da ake ci gaba da yi a yankin, na kara sanya fargabar yiwuwar samun mummnan hadarin nukiliya.
A hannu guda kuma, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana cewa Jamus na ci gaba da taimakawa sojojin Ukraine a yakin da suke da Rasha. A cewarsa Jamus din ta bai wa Ukraine manyan makamai da suka hadar da tankar yaki samfurin FlaK tank Gebard, wadda ke bayar da kariya daga hare-hare ta sama. Scholz ya bayyana hakan ne, yayin wata ziyara da ya kai sansanin bayar da horo ga sojojin Ukraine kan amfani da tankokin yaki a yankin Putlos kusa da birin Oldenburg a jihar Schleswig-Holstein da ke arewacin Jamus.