Zargin Pretoriya da aike wa Rasha makamai
May 11, 2023Talla
Da yake hira da maneman labarai kan batun jakadan Amurka Reuben Brigety ya ce Washington na da tabbacin cewar wani jirgin ruwa dauke da kayan yaki ya bar tashar jiragen ruwan sojan kasar Afrika ta Kudun a watan Disamban bara inda ya nufi Rasha shake da makaman.
A lokacin da majalisar dokokin Afrika ta Kudu ta nemi shugaba Cyril Ramaphoza da ya yi mata karin bayani kan jirgin ruwan mai lakabi da Lady R da ake batu, ya ce ana ci gaba da bincikar batun kuma lokaci na zuwa da zai ba da haske a kai.
Afrika ta Kudu dai na da kyakkyawar alaka da Rasha, kuma ko da a watan Faburairun da ya gabata kasar ta karbi bakuncin wani atisayen sojoji na hadin gwiwa wanda Rasha da China suka shirya ana daf da cika shekara guda da fara yakin Ukraine.