1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin amfani da guba a rikicin Siriya

April 4, 2017

Ana zargin gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta Siriya da amfani da sinadari mai guba cikin yakin basasan kasar abin da ya janyo mutuwar kimanin mutane 60.

https://p.dw.com/p/2aefP
Syrien Idlib Giftgas Angriff
Hoto: picture alliance/dpa/M.Karkas

Gwamnatin Faransa ta kira taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da zargin amfani da sinadari mai guba da gwamnatin Siriya ta yi cikin yankin arewa maso yammacin kasar da ke hannun 'yan tawaye, lamarin da ya janyo mutuwar mutane kusan 60, kana wasu 200 suna cikin mawuyacin hali na rashin lafiya.

'Yan gwagwarmaya suna zargin gwamnati Siriya da watsa sinadaran lokacin da suka kai farmaki ta sama cikin lardin na Idlib. Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya kira takwaransa na Rasha Vladimir Putin domin nuna takaici kan matakin gwamnatin Siriya mai samun goyon bayan Rasha kan amfani da sinadarin mai guba. Tuni kungiyar Tarayyar Turai ta ce Shugaba Bashar al-Assad na Siriya ake zargi da amfani da sinadari mai guba kan 'yan kasarsa.