1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe na zargin Koriya ta Arewa da tauye 'yanci

December 12, 2020

Kasashen duniya duniya guda takwas ciki har da Jamus da Amirka sun zargi Koriya ta Arewa da amfani dokar kulle ta corona wurin ci gaba da take hakkin dan Adam.

https://p.dw.com/p/3mcpf
Nord Korea | Rede von Kim Jong Un
Hoto: Reuters/KCNA

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan gudanar da taron kwamitin sulhu na MDD a ranar Jumma'a. 

Kasashen  da suka hada da Jamus da Belgium da Dominican Republic da Estonia da Faransa da Birtaniya da Amirka da kuma Japan sun hadu sun yi baki daya, sun zargi Koriya ta Arewa da rufe wa 'yan adawa baki da hana jama'a fadin albarkacin bakinsu da kuma tauye 'yancin addini. Kasashen sun ce Koriya ta Arewa ta yi amfani da dokar kullen coronavirus wurin aiwatar da wadannan munanan laifuka, inda suka ce Koriyan tafi mutumta tsarinta na makamashin nukiliya a kan bukatun mutanen kasar.