Rasha ta musanta hannu a kazamin harin Ukraine
January 17, 2023Talla
Alkaluman wadanda suka mutu a sakamakon wasu muunanan hare-hare da ake zargin Rasha da kai wa kan wani gini a garin Dnipro da ke tsakiyar kasar Ukraine ya zarce 40 a wannan Talata, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da binciken baraguzan gini da fatan gano wasu karin mutane 25 da suka bace tun bayan hare-haren da ake ganin, sune mafi muni da Rasha ta kai tun bayan soma mamayar Ukraine.
A jawabinsa, Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ya ce, an kai su da makamai masu linzami yana mai cewa, Rasha ta tafka laifin yaki da ke bukatar daukar matakin shari'a a kanta. Kawo yanzu dai, gwamnatin Kremlin ta musanta zargin cewa ita ta kai wadannan hare-haren na ranar Asabar da ta gabata.