Zargin 'yan jarida da cin amanar Yuganda
November 23, 2017Talla
Editoci da daraktoci takwas na gidan wata fitacciyar jarida a kasar Yuganda an tuhumesu da laifi na cin amanar kasa bayan da jaridarsu ta fitar da wani labari da ya zargi hannun Shugaba Yoweri Museveni a kokarin shirya kifar da takwaransa na kasar Ruwanda Paul Kagame, kamar yadda lauya da ke kare shugaban ya bayyana a wannan rana ta Alhamis.
Mutanen takwas an kamasu a ranar Talata lokacin da 'yan sanda suka kai wani simame gidan jaridar ta Red Pepper da ke watsa labaransa a harshen Ingilishi da ma harshen da al'ummar kasar ke amfani da shi. A ranar Laraba kuma aka tuhumesu da laifi na cin amanar kasa, laifin da ka iya kaisu ga gidan kaso tsawon shekaru bakwai. Ko da yake sun musanta.