1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin yunƙurin kai hari akan ofisoshin jakadancin Girka

November 1, 2010

'Yan sanda a ƙasar Girka sun tsare wasu mutane biyu bisa zargin kokarin tarwatsa ofishin jakadancin ƙasar da ke ƙetare

https://p.dw.com/p/PvrY
Ginin gidan tarihi a birnin Athens na GirkaHoto: Hellenic Ministry of Culture

Jami'an 'yan sanda a ƙasar Girka sun tsare wasu mutane biyu a wannan Litinin, bayan da suka bankaɗo cewar suna yunƙurin ƙaddamar da hare hare ga ofisoshin jakadancin ƙasar guda ukku dake ƙetare, inda kuma suke ɗauke da sinadaran yin haka cikin wani ƙunshi da kuma ɗayan da aka nufi kaiwa shugaba Nikolas Sarkozy na ƙasar Faransa. Ƙunshi ɗaya da aka nufi tarwatsa ofishin jakadancin Girka a ƙasar Mexico ya fashe ne a lokacin da jami'ai ke gudanar da bincike, inda ya ƙona ɗaya daga cikin ma'aikata.

Hukumomin suka ce sun tsare mutanen biyu ne a wani kamfanin aika saƙonnin kayayyaki, ɗauke da wasu abubuwan da za su iya tarwatsewa, waɗanda aka nufi kaiwa shugaban Faransa da kuma ofisoshin jakadancin ƙasashen Beljiam da kuma na Holland da ke birnin Athens, fadar gwamnatin ƙasar ta Girka. 'Yan sandan suka ce mutane biyun da ake zargin, suna riƙe da ƙananan bindigogi, kana ɗayan su yana sanye da rigar bada kariya ga harsashin bindiga.

Hakanan bayanai na nuna cewar waɗanda ake zargin, shekarun su na haihuwa ya ɗara 20 20, kuma an yi amannar cewar mambobin ƙungiyar masu matsanaicin ra'ayin da mafi yawan lokuta akan fassara sunan su da cewar gungun masu wasa da wuta ne.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu