Zartar da hukuncin kisa a Iran
October 28, 2024Talla
Wata sanarwa da hukumomin shari’a a Iran suka fitar, ta ce bayan yin nazari bisa shari’ar da aka yi, a safiyar wannan Litinin mahukuntan sun bada izinin zartar da hukuncin kamar yadda kotu ta yanke. Dama tun a shekara ta 2020 da aka sameshi da laifi kuma tun wannan lokacin Jamshid Sharmahd yake zama a gidan yari kafin hukumomi su zartar da hukucin a wannan Litinin. Kasar Iran na cikin kasashen duniya da har yanzu ke zartar da hukuncin kisa. Masu kare hakkin jama'a da 'yan fafitika, sun jima suna gangami a Iran da kuma musamman a kasar Jamus don neman a sako Jamshid Sharmahd daga gidan yari, abin da bai samu ba har izuwa wannan Litinin da aka zartar masa da hukuncin kisa kamar yadda a baya kotu ta bada umarni.