Zartar da hukuncin kisa a Masar
January 2, 2018Kazalika gwamnatin kasar ta sake tsawaita zangon dokar ta bacin da aka fara sawa a lokacin da aka kai wa wasu Coci wani mummunan hari a watan Afrilun bara, dokar da shugaba Abddel Fattah el Sissi ya kafa a halin yanzu za ta cigaba da aiki har na tsawon watanni uku
Ita dai kasar ta Masar ta yi fama da kungiyar ta'addanci ta IS wacce ke da sansani a yankin Sinai, kuma ta ke kai hare-hare a fadin kasar musamman ma ga jami'an tsaro da kuma mabiya addinin Kirista.
Mummunan harin na shekara ta 2015 ya faru ne a wani filin wasa a birnin Kafr-el-Sheikh, a inda wadansu daliban makarantar horas da sojoji suke jiran motar da za ta kai su makaranta.
Zartar da hukuncin kisan da aka yi wa mutane hudun ta hanyar rataya, an yi shi ne a wani gidan yari da ke garin Alexandria wanda hakan ya kawo adadin wadanda aka samu da laifin ta'addanci kuma aka zartas musu da hukuncin kisa zuwa mutane 19 daga makon daya gabata zuwa yau. Sai dai kungiyoyi da masu rajin kare hakkin 'dan Adam na cewa akwai kura-kurai cikin yadda ake yanke hukuncin .