Zartar da hukuncin kisa a ƙasar Iran
December 28, 2010Kamfanin dillalcin labaran ƙasar Iran wato IRNA, ya rawaito cewa hukumomin ƙasar sun rataye mutumin da aka zarga da yiwa Isra'ila leƙen asiri. Wanda aka ratayen mai suna Ali Akbar Saiadati, kutun jujin juya halin ƙasar ne ta same shi da laifi kuma yanke masa hukunci. Kotun ta samu Saiadati da laifin baiwa ƙungiyar leken asirin Isra'ila ta Mossad bayanai kan ƙarfin sojin Iran da kuma yawan makamai masu linzami da ta mallaka. An samu shaidun cewa mutumin ya sadu da Yahudawan a wani otel dake ƙasar Turkiya da Thailand da kuma a ƙasar Hollands inda ya basu bayanan sirri. A watan jiya ne dai wani masanin haɗa nukiliya ɗan ƙasar Iran, ya rasu bayan da aka dasa bam a ƙarƙashin motarsa. Ita dai ƙasar Isra'ila a yanzu bata da abokin gaba a yankin da yakai ƙasar jahmhuriyar Islama ta Iran wanda take ganin na son mallakar makaman nukiliya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Ahmadu Tijjani Lawal