Zaɓen shugaban ƙasa a Laberiya
October 11, 2011A safiyar wannan Talatar ce 'yan Laberiya ke zuwa runfunan kaɗa ƙuri'ar zaɓen sabon shugaban ƙasa. Shugabar ƙasar dake kan mulki a yanzu, wadda ke zama zaɓaɓɓiyar mace ta farkon da ta ɗare kujerar shugabancin wata ƙasa a ɗaukacin nahiyar Afirka, wadda kuma shekarun ta a duniya 72 ne Ellen Johnson Sirleaf, tana fuskantar babban ƙalubale daga Winson Tubman - mai shekaru 70 da haihuwa. Rahotanni suka ce gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan adawar dai ya ƙarfafa ne bayan daya ɗauki tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa a duniyar nan George Weah a matsayin mai rufa masa baya. A ranar Jumma'ar da ta gabata ce Sirleaf ta sami kyautar zaman lafiya ta Nobel. Baya ga 'yan takarar biyu kuma, akwai wasu 'yan takara 14 da za su fafata tare da su wajen neman muƙamin shugaban ƙasar ta Laberiya. Hakanan 'yan Laberiyar za su zaɓi waɗanda za su wakilce su a majalisar dokokin ƙasar a lokacin wannan zaɓen.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman