1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen 'yan majalisa na gaba da wa'adi a Girka a Afrilu

February 13, 2012

Gwamnatin Girka ta sanar cewa za ta shirya zaɓen 'yan majalisa na gaba da wa'adi da zarar ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljuhu da majalisar ƙasa ta amince da su.

https://p.dw.com/p/142pc
Blick auf das Parlamentsgebäude in der griechischen Hauptstadt Athen, aufgenommen am 02.06.2009. Das Gebäude am Syntagma-Platz (Verfassungs-Platz), dem zentralen Platz Athens, wurde 1836 bis 1842 als Residenz für Griechenlands Könige gebaut und ist seit 1934 Sitz des griechischen Parlaments. Direkt davor befindet sich das Grab des unbekannten Soldaten, vor dem zur vollen Stunde eine Wachablösung stattfindet. Foto: Peter Zimmermann +++(c) dpa - Report+++ +++(c) dpa - Report+++
Majalisa ta taka rawa game da tsumin kudi na Girka.Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Girka ta bayyana aniyarta ta gudanar da zaɓen 'yan majalisa na gaba da wa'adi a watan Afrilu mai zuwa idan Allah Ya yarda. Wannan matakin na Athens ya zo ne bayan da gwamnatin Papademos ta ɗibar wa kanta wa'adin wata guda da rabi domin aiwatar da matakan tsuke bakin aljuhu da majalisar dokoki ta amince da su. A watan oktoba mai zuwa ne dai ya kamata wa'adin mulkli na gwamnatin ta rikon kwarya karkashin Lucas Papademos ya zo karshe.

A daren lahadi zuwa litinin ne majalisar Girka ta amince da matakin tsimin kudi domin samun tallafin ceto karo na biyu daga ƙungiyar Tarayyar Turai da kuma Asusun bada lamuni na duniya. Sai dai kuma 'yan kasar ta girka sun shafe kwanaki suna zanga-zanga domin nuna rashin jin daɗinsu da matakan tsuke bakin aljuhu da gwamnati ta dauka. Kafafen watsa labaran ƙasar sun nunar da cewa kimanin mutane 120 ne suka ji raunuka lokacin zanga-zangar a birnin Athnes, yayin da masu zanga-zangar suka lalata gine gine da dama, tare da kwasar ganima a wasu shagunan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal