1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Zelensky ya bukaci kasashen yamma su cika alkawarinsu

Binta Aliyu Zurmi
January 12, 2025

Shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine ya yi kira ga kasashe abokan huldarsu da su cika alkawarin da suka dauka na taimakawa Ukraine da makaman da take bukata don kare kanta a yakin da take yi da Rasha.

https://p.dw.com/p/4p4ld
Belgien Brüssel 2024 | Selenskyj gibt Pressekonferenz nach EU-Gipfeltreffen
Hoto: John Thys/AFP

Shugaba Zelensky ya ce a yan kwanankin baya-bayan nan Rasha ta kara kaimi a hare.haren da take kai musu, wanda ya ce sama da rokoki 700 da jirage marasa matuka 600 ne aka harbo su daga yankunan Rasha ya zuwa cikin kasar.

Shugaban na Ukraine ya ce matsayar da aka cimma a taron kungiyar tsaro ta NATO a Washington da kuma na Ramstein na kasar Jamus don  samar musu da makaman kare sararin samaniya har yanzu shiru suke ji. 

Ko a wannan makon Shugaba Volodmyr Zelensky ya ce ya tattauna batun baiwa kasarsa damar sarrafa makamanta na kare sararin samaniya da ma masu linzami.
 

Karin Bayani:Rasha ta kai wa Ukraine kazamin hari da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka