1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zelensky ya yi jawabi ga majalisar Amirka

Abdoulaye Mamane Amadou
March 16, 2022

A yayin da Rasha ke cigaba da mamaya a Ukraine Shugaba Volodymyr Zelensky ya yi jawabi a gaban majalisar dokokin Amirka ta bidiyo, inda ya bukaci taimakon Amirka wajen kare 'yan Ukraine.

https://p.dw.com/p/48agp
Standbild aus der DW TV News Sendung Zelenskyy accuses Russia of genocide in hospital bombing
Hoto: Office of the President of Ukraine (via AP)

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi kira ga takwaransa na Amirka Joe Biden da ya kasance jagoran duniya kuma jagoran zaman lafiya, yana mai jaddada fatan ganin Amirka da kasashen yamma sun ceto Ukraine daga mamayar Rasha.

Shugaba Zelensky na kalaman ne a yayin wani jawabin da ya yi a gaban majalisar dokokin Amirka ta kafar bidiyo a wannan Laraba, inda ya bukaci majalisar da ta karfafa wa yunkurinsa na ganin an kafa wa Rasha takunkumin shawagin jirage a sararin samaniyar Ukraine, a wani mataki na kare 'yan kasar daga luguden wutar da Rasha ke yi.

"A yau yakin da al'ummar Ukraine ke yi suna yi ne ba don kare kasar kadai ba, a'a muna yaki ne da sadaukar da rayukanmu dan kare martabar nahiyar Turai da ma duniya baki daya."

Shugaban ya bayyan cewa yana da bukatar kare sararin samaniyar kasarsa, kuma yana tsananin bukatar taimakon 'yan majalisar dokokin ta Amirka.