Zelensky zai gana da shugabannin EU
February 3, 2023Shugabar hukumar Turai Ursula von der Leyen da kuma shugaban majalisar gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai Charles Michel za su gana da shugaban kasar Ukraine Volodmyr Zelensky a birnin Kyiv. Shugabannin biyu za su tattauna ne kan kokarin da Ukraine din ta ke yi na shiga kungiyar ta EU kamar yadda Shugaba Zelensky ya bukata. Sai dai kuma EU ta ce akwai tarin matakai da za a bi kafin Ukraine ta samu damar zama mamba a kungiyar.
Sai dai ana sa rai shugabannin su tattauna batun takunkuman da EU ta kakkaba wa Rasha yayin da kungiyar ke shirin bayyana sabbin takunkuman da za ta kakaba mata a daidai lokacin da ke dab da cika shekara guda da fara yakin. Sauran batutuwan da za su tattauna sun hada da tallafin kudi da kuma makamai ga Ukraine da ma yunkurin ci gaba da fitar da abinci da kuma tallafin sake gina kasar da kuma shirye-shiryen zaman lafiyarta.