1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Zelensky a Amurka

Zainab Mohammed Abubakar
December 21, 2022

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine na shirin fara ziyara a birnin Washington, ziyarar da za ta kasance irinta ta farko a ketare tun bayan da Rasha ta kai mamaya kasarsa.

https://p.dw.com/p/4LGNH
Volodymyr Zelensky
Hoto: AFP/Getty Images

A wannan Larabar ce a ke saran shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine zai kai ziyara a birnin Washington, ziyarar da za ta kasance irinta ta farko a ketare tun bayan da Rasha ta kai mamaya kasarsa, a cewar kafafen yada labaran Amurkan, ba tare da ayyana majiyarsu ba.

Rahotanni na nuni da cewar shugaban na Ukraine zai gana da Shugaba Joe Biden a fadar gwamnati ta White House, kana daga bisani yayi jawabi a gaban 'yan majalisar Amurkan.

A yayin ziyarar ta Zelensky kazalika, ana saran Amurkan ta sanar da bai wa Ukraine tallafin nau'rorin kare hare-hare ta sararin samaniya, wadda Kiev za ta yi amfani da su wajen kare kanta daga harin jiragen yaki da makamai masu linzami ko da kuwa daga nesa aka harba.