1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zelenskyy na Ukraine ya mutunta Narendra Modi na Indiya

Mouhamadou Awal Balarabe
August 23, 2024

Firaministan Indiya Narendra Modi ya kai ziyarar aiki kasar Ukraine da nufin sasanta rikicin da ke tsakanin kasar da Rasha tare da karfafa huldar tattalin arziki da hadin gwiwa a bangarorin tsaro da kimiyya da fasaha.

https://p.dw.com/p/4jqKo
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ne ya tabri firaministan Indiya Narendra Modi
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ne ya tabri firaministan Indiya Narendra ModiHoto: Indian Prime Minister’s office/AP/picture alliance

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da kansa ne ya tarbi Narendra Modi a birnin Kyiv, kasancewa shi ne shugaban gwamnatin Indiya na farko da ya ziyarci Ukraine domin karfafa dangantakar tattalin arziki da hadin gwiwa a bangarorin tsaro da kimiyya da fasaha. Modi ya kai wannan ziyarar birnion Kyiv, wata daya da rabi bayan da ya ziyarci Rasha da ta mamaye Ukraine, matakin da Shugaban Ukraine ya yi kakkausar suka akai.

Ita dai Indiya da ke da kyakkyawar alaka da Moscow ta ki fitowa fili ta yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine, inda a maimakon haka take karfafa tattaunawa da diflomasiyya tsakanin Rasha da Ukraine don warware rikicin da ke tsakaninsu. Dama dai tun a jiya alhamis a kasar Poland, Narendra Modi ya bayyana cewar babu wani rikici da za a iya warware shi a fagen yaki.