1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda na tsare da Mutasa

Zainab Mohammed Abubakar
October 11, 2018

Rundunar 'yan sandan Zimbabuwe ta cafke Peter Mutasa da wasu masu fafutukar neman 'yanci, gabanin shirin gudanar da jerin gwano adawa da barkewar cutar Kwalara da durkushewar tattali

https://p.dw.com/p/36Mil
Simbabwe, Harare: Angst vor Cholera
Hoto: picture-alliance /S. Jusa

Mai magana da yawun lauyoyin kare hakkin al'umma Junbirai Mafunda, ya fada wa kamfanin dillancin labaru na Faransa AFP cewar, Peter Mutasa da ke shugabantar kungiyar kwadago mafi girma a Zimbabuwen mai suna  ZCTU a takaice, na daga cikin mutanen da 'yan sanda ke tsare da su.

A wannan Alhamis din ce dai Mutasa ya kira gangamin adawa da gwamnati a babban birnin kasar watau Harare, biyo bayan barkewar annobar cutar Kwalara.

Kungiyar kwadagon kazalika na shirin gudanar da gangamin kasa baki daya dangane da hauhawan farashin kaya da sabon tsarin haraji da aka dorawa kayayyakin masarufi, da halin-ni-'yasu da al'ummar Zimbabuwen suka tsinci kansu a ciki.