1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ci gaba da asarar rayuka a Zirin Gaza

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 29, 2023

Ma'aikatar Lafiya ta Zirin Gaza da Hamas ke iko da shi ta sanar da cewa kimanin mutane dubu 21 da 507 ne suka halaka, tun bayan barkewar yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar ta Hamas da ke gwagwarmaya da makamai a yankin.

https://p.dw.com/p/4ahx4
NGabas ta Tsakiya | Rikici | Isra'ila | Hamas | Zirin Gaza | Asarar Rayuka
Ana ci gaba da asarar rayuka a yankin Zirin Gaza na FalasdinuHoto: Mohammed Talatene/dpa/picture alliance

Ma'aikatar Lafiya ta yankin na Zirin Gaza da Hamas din ke iko da shi, ta nunar da cewa cikin wadandan suka halaka har da wasu 187 da suka rasa rayukansu sa'o'i 24 da suka wuce. Haka kuma ta ce wasu dubu 55 da 915 sun jikkata, a yakin da kawo yanzu aka kwashe tsawon makonni 12 ana gwabza shi. Hukumar ula da 'Yan Gudun Hijirar Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA ta wallafa a shafinta na X cewa, akwai mutane 308 da ke neman mafaka a wajensu da suka halaka a yakin kana wasu 1,095 sun jikata yayin da suke sansanonin da suka kafa doamin masu neman mafakar. Isra'ilan dai ta sha alwashin murkushe 'yan kungiyar Hamas a doron kasa, tun bayan harin ba-zatan da ta kai mata a ranar bakwai ga watan Oktobar wannan shekara da ya janyo wannan balahira. Yayin harin dai, Hamas din ta yi garkuwa da mutane 250 kana wasu 1,140 suka halaka.