Ziyara Angela Merkel a Afghanistan
November 4, 2007Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta kai ziyara aiki ta farko a ƙasar Afghanistan.
Bayan tattanawa da hukumomin ƙasar, Merkel ta kuma gana da rundunar sojojin Jamus da ke Mazar-i Charif domin ƙara mata ƙarfin gwiwa.
A watan da ya gabata Majalisar Dokokin Bundestag, ta kaɗa ƙuri´ar amincewa da ƙara wa´adin rundunar da shekara 1, duk kuwa da adawar da jamusawa ke nunawa a game da hakan.
A lokacin da ta ke bayyani bayan wannan ziyara, Merkel na cewar.
„Ina matukar farin ciki da tantanawaer da na yi tare da sojojinmu, sun kuma bayana gamsuwa, a game da talllafin da su ke badawa, ta fannin samar da zaman lahia mai ɗorewa a ƙasar Afghanistan.
A `yan makwani masu zuwa, za mu sake gabatarwa Majalisar Dokoki sabin bukatoci, a game da ayyukan rundunar.“
Ya zuwa dai Jamus ta yi asara sojoji 26, a cikin hare-haren yanTaliban na ƙasar Afghanistan.