Ziyara Angeller Merkel a gabas ta tsakiya
April 1, 2007Shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkel,na ci gaba da ziyara aiki, a yankin gabas ta tsakiya.
Bayan tantanmawr da ta yi jiya, da Sarki Abdalah na Jordan, a yau ta gana da Praministan Isra´ila Ehud Olmert, dac kluma shugaban hukumar Palestinawa Muhamud Abbas.
shugabar ƙungiyar gamayar turai, ta yi kira ga ɓangrorin 2, su ƙudurci aniyar samar da zaman lahia a yaƙin da ya ƙi ci, ya ƙi cenyewa tsakanin su.
Merkel, ta buƙaci sabuwar gwamnatin Palistinu, ta yi anfani da shawarwarin da ƙasashen masu shiga tsakanin rikicin gabas ta tsakiya su ka shinfiɗa, wajen yunƙurin warware rikicin Isra´ila da Palestinu.
Wannan shawarwari, sun tanadi Palestinu, ta amince da Isra´ila a matsayin hallataciyar ƙasa, ta kuma dakatar da kai mata hare -hare.
Merkel ta ce ƙungiyar gamayya turai a shire ta ke,ta bada cikkaken goyan baya ga gwamnatin Palestinu, muddun ta cika wannan sharruɗa.
A ɗaya wajen ta bayyana gamsuwa da yunƙurin ƙasashen larabawa na kawo ƙarshen rikicin gabas ta tsakiya.
Shugabar gwamnatin Jamus ta ɗauri aniyar gudanar da aiki tuƙuru,domin shinfiɗa sabin hanayoyin cimma massalaha, a rikicin Isra´ila da Palestinu, kamin ƙarshen wa´adin ta, na shugabancin ƙungiyar gamayya turai, a watan juni mai zuwa.