Ziyara Angeller Merkel a India
October 30, 2007A yammacin jiya shugabar gwamnatin Jamus Angeler Merkel, ta sauka a birnin New Delhi na ƙasar India, inda ta fara ziyara aiki ta kwanaki 4.
Tawagogin ƙasashen 2, za su anfani da wannan dama, domin masanyar ra´ayoyi a kann batutuwa daban-daban, da su ka shafi tattalin arziki da siyasa.
A wannan rangadi irin sa na farko a ƙasar India, shugabar gwamnatin Jamus na tare da rakiyar ministar ilimi zurfi da kuma jami´in hukumar tattalin arzikin ƙasar Jamus.
A game da haka, tawagogin 2 za su maida hankali, a kann batuwan da su ka jiɓanci ilimi, da kuma saye da sayarwa.
India da ake wa taken babbar demokratiyar dunia, na kann hanyar ta, ta bunƙassar tattalinarziki da kuma samin ƙarfin faɗa aji a fagen siyasar dunia.
Bayan yarjenijiyar da ta rabawa hannu tare da Amurika ta fannin bunƙasar makashin nuklea, India da taka kyaukyawar rawa ta fannin hada-hadar kasuwwanin dunia da kuma yaƙi da ɗumamar yanayi, wanda halin yanzu ke tsaka tsakiyar mahaurori a manyan fadodin mulkin na ƙasashen dunia.
Sannan India tare da Jamus, na daga ƙasashen da ke fafatakar samun kujera dindindin a komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia.
Ziyara ta Angeler ta Angeller Merkel wata dama ta tantanawa a game da dukkan wannan batutuwa, kamar yadda Saurabh Shukla, na jaridar India Today ya bayyana.
„Mahimman batutuwan da su maida hankali akai su ne na cuɗe ni in cuɗe ka tsaknaijnkasashen 2.
Jamus da India nada ra´ayoyi iri daya, a game da yaki da ta´danci.
To amma a ganina, mu´amila a tsakanin su na buƙatar ƙarin ƙarfi mussamman a matsayin Jamus na jagorar ƙasashen turai“.
Mu´amila tsakanin Jamus da India, ta ƙunshi al´amuran da su ka shafi demokradiya, da kare haƙin bani adama, sannan ƙasashen 2 za su anfani da ziyara Angeller Merkel, domin yin bitar halin da su ke ciki, ta wannan fanni da dai sauran al´amarunda su ka shafi ƙasashen inji Navtej Sarna mai baiwa ministan harkokin wajen India shawara.
„Tun shekara ta 2001 Jamus da India su ka ƙulla yarjeniyoyi masu ƙarfi, ta fannoni da dama, alaml misali ɓangaren demokraɗiya.
Bayan haka, mu da ra´ayoyi iri ɗaya wajen gudanar da kwaskwarima ga komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia,da kuma yaƙi da ta´adanci“.
To amma a cewar ɗan jaerida Saurabh Shukla, a yanzu fa dunia ta ci gaba, a game da haka, ya zama wajibi ga India da Jamus su ɓullo da wani saban babe na huldodin tsakanin su.
„ Ya kamata mu lalubo wasu sabin hanyoyin mu´amila.
India da Jamus ƙasashe ne wanda ke da hulɗa mai ƙarfi,kuma mai yawa, to amma a halin yanzu akwai da dama daga ƙasashen turai da su ka kutso kai a India , har ma su ka fi Jamus samun gidin zama.“
Bayan saye da sayarwa, diplomatia da siyasa, Jamus na da hulɗoɗi ta fannin ilimi tare da India, domin a yanzu haka akwai a ƙalla ɗallibai dubu 4, yan asulin India da ke samun horo a makarantu daban-daban na Jamus.
„