1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara C. Rice a yankin Gabas ta tsakiya

Yahouza S. MadobiSeptember 20, 2007

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice ta gana da hukumomin Isra´ila da na Palestinu

https://p.dw.com/p/BtuX
Hoto: AP

A ci gaba da rangadin da ta ke a yankin gabas ta tsakiya, sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta gana a sahiyar yau da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas a birnin Rammallah.

Wannan ganawa ta biwo bayan wata makamanciyar ta da Condoleesa Rice ta yi da hukumomin Isra´ila tsakanin jiya da sahiyar yau..

Kamar a cen Isra´ila a Rammallah ma, RIce, ta tantana da shugaban hukumar Palestinawa, a game da batutuwan da su ka jiɓanbici yunƙurin samar da zaman lahia a yankin gabas ta tsakiya.

Wannan shine karo na 6, da ta kai ziyara a ƙasashen 2 daga farkon shekara da mu ke ciki zuwa yanzu.

Jim kaɗan bayan ganawar ta shugaba Mahamud Abbas, Condoleesa ta bayana fari ciki, a game da turbar da aka hau ta kawo ƙarshen rikicin gaba s ta tsakiya:

Wannan lokaci inda nike da ɗauke da kyaukyawan zato na cimma burin da a ka sa gaba, sakamakon aiki tuƙuru da mu ka yi.

Saidai har yanzu akwai sauran rina kaba ta la´akari da matsalolin da ke gittawa.

Amma a gaskiya, bayan na ji ta bakin hukumomin Isra´ila da kuma na Palestinu na kara samun ƙarfin gwiwa“.

Ɗaya daga mahimman matsalolin da su ka gitta sun haɗa da sanarwar da Isra´ila ta bayyana a jiya, inda ta ɗauki zirin Gaza, a matsayin wani sansani, wanda zata ƙadamar da yaƙi a cikin sa, matakin da hukumomin Palestinu da ma na sauran ƙasashen larabawa su ka yi Allah wadai da shi.

A ɗaya wajen Condolesa da Mahamud Abbas, sun tantana a game da taron ƙasa da ƙasa, wanda Amurika ta buƙaci shirya, a game da rikicin gabas ta taskiya.

A cewar Mahamud Abbas, wanda taro zai kasance matsayin tubali mai ƙarfi na girka ƙasashen 2, wato Isra´ila da Palestinu, wanda za su maƙwabtaka cikin girma da arziki, a maimakon tashe-tashen hankulla.

Mahamud Abbas ya buƙaci Amurika ta matsa lamba ga ƙasar Isra´ila domin kawo ƙarshen ƙiƙi-ƙaƙa da ta hana ruwa gudu ga batun zaman lahia a wannan yanki, mussamman matsalolin iyakokin tsakanin Isar´ila da Palestinu, matsayin birnin Qudus, da batu mai sarƙƙaƙiya na mamayen da Isra´ila ta yi a yankunan Palestinawa ,sai kuma marsalar yan gudun hijira.