Ziyara C. Rice da R. Gates a gabas ta tsakiya
July 30, 2007Nan gaba a yau ne sakatariyar harakokin wajen Amurika,Condoleesa Rice, da takwaran ta na tsaro, Robert Gates, za su fara wani rangadi a gabas ta tsakiya.
Ɗaya bayan ɗaya, za su ziyarci Masar, Saudi Arabia, da kuma Isra´ila da Palestinu.
Mahimman batutuwa da za su tantana a kai, sun haɗa da rikicin Irak, da kuma halin da ake ciki, a yunƙurin cimma massalaha, a rikici tsakanin Isra´ila da Palestinu.
Minitstocin 2, za su anfani da wannan dama, domin rattaba hannu a kann wata yarjejeniyar bada tallafin kuɗaɗe ga Isra´ila, wanda yawan su ya kai dalla milion dubu 30.
A ɗaya wajen, Amurika ta bayyana bada goyan baya ga shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, a game da matakin da ya ɗauka na girka sabuwar gwamnati, bayan Hamas ta mamaye zirin Gaza.
Kazalika Amurika ta alƙawarta bada ƙarfin gwiwa ga Isra´ila da Palestninu a sabuwar tantanawar da su ka shiga, da zumar kawo ƙarshen baddaƙalar da ta ƙi ci, ta ƙi cenyewa tsakanin su.