Ziyara Condoleesa Rice a gabas ta tsakiya
October 2, 2006Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice ta kai ziyara aiki a yankin gabas ta tsakiya.
A matakin farko na wannan ziyara, zata gana da Sarki Abdallah na Saudiya, inda za su tantana batutuwa daban-daban da su ka jiɓanci halin da ake ciki a yanki.
Musamman za su maida hankali a kan rikicin makaman nuklear ƙasar Iran, da kuma rikicin Isra´ila da Palestinu sannan da tashe tashen hankulla ƙasar Iraki.
A dangane da rikicin nukleyar Iran ,Rice ta sanar manema labarai cewa, jim kadan kamin tashinta daga Amuruika,ta tantana ta wayar talho, da takwarorinta, na ƙasashe masu kujerun didindin, a komitin sulhu na MDD, da kuma na Jamus, a game da sabuwar hanyar da za su bi domin ɓulkowa wannan taƙƙaddama.
Bayan Saudi Arabia, Condolesa Rice zata ziyaraci Masar , sai kuma Isra´ila da Palestinu.