Ziyara Condoleesa Rice a kasar Ukraine
December 7, 2005Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, na ci gaba da ziyara aiki a nahiyar turai, bayan kasashen Jamus da Rumania, a yanzu haka ta kasar Ukranaine, inda ta gana da shugaba kasa Viktor Ioutchenko.
Rice, ta yabawa hukumomin Ukraine, a game da nasarar da su ka cimma, ta girka demokradiyya.
A ganawar ta shugabar gwamnatin Jamus Angeller Merkel Condoleesa Rice, ta bukaci Jamus, ta taimakawa kasashen gabancin rurai su girka demokradiya, da kuma hita daga kangin talaucin da su ke fama a ciki.
Ta bayyanawa shugaba Ioutchenko cewar, gwamnatin Amurika na bi sau da kafa, yadda harakoki ke gudana a kasar sa, saidai duk da nasarorinda a ka cimma akwai bukatar a kara karfi ta fannin yakar martsalolincinhanci da rashawa.
Nan gaba a yau ne, Condoleesa Rice, zata tashi zuwa birnin Brussels, na kasar Belgium, inda zata halarci taron kungiyar tsaro ta NATO.
Babban batutuwan da za a ztanatanaw a taronsun hada da zargin da a kawa hukumar leken assiri ta Amurika, a game da anfani da filayen jiragen samnar wasu kasashennturai a assurce domin jigilar prisonin da Amurikan ke tuhuma da aikata ta´adanci.