Ziyara Fraministan Isra'ila a ƙasar Girka
August 17, 2010Friministan ƙasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana kyaukkyawan fatan cewa na ba da daɗewa za a koma ga yin shawarwarin gaba da gaba na wanzar da zaman lafiya tsakanin Palasɗinu da Isra'ila.
Netanyahu da ke magana a sa'ilin ziyara da ya kai a birnin Athens na ƙasar Girka, ya ce a shirye suke su je birnin alƙahira, da washinton domin tattauna butun shirin na zaman lafiya.
friministan na Isra'ila wanda ya fara ziyara a ƙasar Girka a jiya litinin na kokarin neman samu wata sabuwar hulɗa ne a yankin na mediteranien, bayan rashin jituwar da ta auku tsakanin Isra'ila da ƙasar Turkiya a watannin da suka gabata.
wannan dai ita ce ziyara ta farko da wani shugaban Isra'ilan ya ke yi a ƙasar Girka wacce ke da allaƙa dakuma hulɗa da ƙasashen larabawa.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu