Ziyara Franck Walter Steinmeir a gabas ta tsakiya
September 7, 2006Ministan harakokin wajen Jamus, Franck Walter Steinmeir, na ci gaba da ziyara a yankin gabas ta tsakiya.
A yamacin yau ya tantana, da hukumomin Beyruth, a game da guddumuwar Jamus, a yunƙurin sake gina Libanan da yaƙi ya ma, kaca kaca.
Ministan, na tare da tawagar ƙurraru ta fannin ayyukan custum, wanda su ka masanyar ra´ayoyi da takwarorin su na Libanon a game da hanyoyin tafiyar da aiki, a filayen saukar jiragen sama.
Jamus ta bayana aniyar kula da ɓangaren sojojin ruwa na rundunar shiga tsakakni, da Majalisar Dinkin Dunia ta yanke hukunci aikawa a libanon.
Hukumomin Berlin, sun yi hakan domin amsa gayyatar da Libanon ta yi masu, ta hanyar MDD.
A yau ne, Isra´ila ta bayana cire takunkumin da, ta saka, na hana zirga zirga a Libanon, bayan ta samu tabas, daga Majalisar Dinkin Dunia, na hana jigilar makammai, zuwa Hizbullahi daga ƙasashen ketare.
Bayan Kasar Libanon, Steinmeir ya ziyarci Isra´ila domin ci gaban wannan tantannawa.