1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Havier Solana a yankin gabas ta tsakiya

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueY

Idan an jimma kaɗan a yau, sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai, Havier Solana zai tantana da shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas.

Solana, ya fara wani saban rangadi na kwanaki 6, a yankin gabas ta tsakiya, da zumar farfaɗo, da batun sulhu tsakanin Isra´la da Palestinu.

Kazalika, zai anfani da wannan dama, domin issar da kira ga ƙungiyoyin Hamas da na Fatah, su ba maraɗa kunwa, ta hanyar cimma daidaiton girka gwamnatin haɗin kan ƙasa, kamar yadda su ka ambata.

Ziyara Solana, ta zo a daidai lokacin da, rikikci ya yi tsamari, tsakanin ƙungiyoyin 2 na Palestninu, masu gaba da juna.

A matakin farko na wannan rangadi, Havier Solana, ya tantana jiya, da praministan Isra´ila Ehud Olmert.

Sannan, zai ziyaraci ɗaya bayan ɗaya, ƙasashen Lebanaon, Jordan da Masar.