1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara H.Solana a gabas ta tsakiya

September 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuCZ

A ci gaba da neman hanyoyin warware rikicin gabas ta tsakiya, yau ne sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamaya turai, Havier Solana, ya fara rangadi na kwanaki 2, a Isra´ila da Palestinu.

Jim kaɗan kamin fara tantanawa da Praminista Ehud Olmert na Isra´ila a birnin Qudus, Solana ya bayyana buƙatar cimma matsaya guda, a game da taron ƙolin da Amurika ta gayyata, wanda zai maida taska, a kann laluben hanyoyin warware rikicin yankin.

Nan gaba a yau, Havier Solana,zai gana da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, da Praminista Salam Fayyad.

Sai kuma gobe ,ya sadu da ministocin tsaro da na harakokin wajen Isra´ila.

Wannan rangadi na wakana a daidai lokacin da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya rattaba hannu a kann wata doka, wada ta tanadi kwaskwarima, ga kundin tsarin zaɓe a ƙasar.