Ziyara Kodolisa Rice a yankin gabas ta tsakiya
November 14, 2005Sakatariyar harakokin wajen Amurika Kondolisa Rice na ci gaba da ziyara aiki a yankin gabas ta tsakiya.
Nan gaba a yau Rice zata gana da praministan Isra´ila Ariel Sharon, da kuma shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas, da zumar karfafa zaman lahia tsakanin kasashen 2.
Kondolisa Rice zata tantanna da Sharon a game da batun amfani da taswirar zaman lahia , da kuma dakatar da ginin sabin matsugunan yahudawa yan kaka gida a yankunan Palestinu.
Sannan tare da Mahamud Abbas zata tantana a kan batun yaki da kungiyoyin Hamas da na Jihadil Islami, da a ka dauka tamkar masu kafar angullu ga cimma lahia a yankin.
Tunni dai a ranar jiya Praministan Isra´ila ya sanar cewa ba zai koma tantanawa ba, da hukumomin Palestinu muddun ba su magance hare haren da kungiyoyin Hamas da Jihadil Islami ke kaiwa Isra´ ila ba.
Bayan ganawa daban daban, Rice zata ziyarci birnin Kudus, domin halartar tarrurukan cikwan shekaru 10 da mutuwar tsofan Praminista Isra`ila Izak Rabin.
Mataki na gaba a wannan rangadi shine kasar Jordan, inda za ta kai ta`aziyar gwamnatin Amurika a game da hae-r haren kunar bakin wake da su ka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a Amman baban birnin kasar.