Ziyara Merkel a Japan
August 29, 2007Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angeller na ci gaba da rangadi a nahiyar Asia.
Bayan ƙasar Sin, a yau ta sauka Japan, inda ta fara tantanawa da hukumomin Tokyo a game da batutuwa daban daban, da su ka shafi mu´amila ,tsakanin ƙasashen 2,da kuma matsalolin taɓarɓarewar mahhali.
A ganawar da ta yi da praministan Japan Shinzo Abbe , Merkel ta yaba tallafin da Japan ke bayar wa ga rundunar ƙasa da ƙasa a Afghanistan.
A gobe zata gana da shugaban jam´iyar adawa Ichiro Ozawa, wanda ke nuna mummunar adawa ga tallafin sojojin Japan a ƙasar Afghanistan.
A ƙarshen wannan rangadi ranar juma´a, shugabar gwamnatin Jamus, zata gabatar da wani jawabi ,a birnin Kyoto, a game da batun yaƙi da ɗumamar yanayi.