1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Nuri Al-Maliki a ƙasar Iran

September 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bujm

Praministan Irak Nuri-Al Maliki, ya kai ziyara farko, a ƙasar Iran, inda ya gana da shugaban ƙasa Mahamud Ahmadinedjad.

Rahotani daga fadar mulki a birnin Bagadaza, sun ce babban burin wannan ziyara shine, na ƙarfafa dangataka da cuɗe ni -in cuɗe ka, tsakanin ƙasashen 2 masu maƙwabtaka da juna, amma su ka kasance cikin zaman ba ga maciji.

A sakamakon gananawar, shugaban Iran, ya alƙawarta bada taimakon da ya dace, domin tabbatar da zaman lahia a ƙasar Irak, da ke fama da tashe tashen hankulla, tun bayan kifar da shugaba Saddam Hussain.

Shugabanin 2, sun kiri taron manema labarai na haɗin gwiwa, inda su ka bayana sakamakon da su ka cimma.

Baki ɗaya, sun amince, su bada haɗin kai, ta fannin tsaro da tattalin arziki.

Nan gaba a yau, Nuri Al-Malilki, zai gana da shugaban Majalisar Shura ta ƙasa ,Ayatollah Ali Khameni, da kuma tsofan shugaban ƙasa Akbar Hashemi Rafsanjani.