Ziyara shugaban Iran a Sudan
March 2, 2007Talla
Shugaban ƙasar Iran Mahamud Ahmadinedjad na ci gaba da ziyara aikin ,da ya kai da a ƙasar Sudan.
A sakamakon ganawar da yayi ,da shugaba Omar El-Bashir, sun cimma daidaito a kan hanyoyin bunƙasa cuɗe ni cuɗe ka, tsakanin ƙasashen su 2, ta fannoni daban-daban na rayuwa.
Sudan da Iran, a halin yanzu, sun kasance ƙasashen da ke kanun labarun a dunia, ta la´akari da kafawar wando guda da su ka shiga ,da Amuriak da kuma Majalisar Dinkin Dunia.
Bayan ƙasar ta Sudan, gobe idan Allah ya kai mu, Mahamud Ahmadinedjad, zai fara rangadi a ƙasar Saudi Arabia.
Zai anfani da wannan dama, domin tantanawa da hukumomin ƙasa mai tsarki, a game da rikicin gabas ta tsakiya, da kuma taƙƙadamar makaman nuklea.