Ziyarar Angela Merkel a Turkiyya
October 5, 2006A ziyarar da ta kai a Turkiyya, shugabar gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel ba ta cim ma kusantar juna da takwararn aikinta na birnin Ankara, Tayyip Erdogan ba, a kan batun tattaunawar da ake yi ta shigar Turkiyyan cikin Ƙungiyar Haɗin Kan Turai. Ɓangarorin biyu dai sun sami saɓani ne kan batun hana jiragen sama da na ruwan Cyprus da Turkiyyan ta yi, wajen yin amfani da kafofinta. Wannan rikici da ƙungiyar EU da Turkiyya ke yi kan Cyprus ɗin dai zai iya zamowa wani shinge ga ci gaban tattaunawar shigar Turkiyyan cikin ƙungiyar. A farkon ganawar da ta yi da Firamiyan Turkiyyan yau a birnin Ankara, Merkel ta ƙarfafa cewa, ɓangaren Girkawa ta tsibirin Cyprus dai, wato mamba ce ta ƙungiyar Haɗin Kan Turai. Sabili da haka, dole ne Turkiyyan ta bi ƙa’idojin yarjejeniyar birnin Ankara, wadda ta bai wa duk ƙasashen ƙungiyar damar yin amfani da tashoshin jiragen ruwa da filayen jirgin samanta. Sabili da haka kamata ya yi, Turkiyyan ta buɗe ƙofofin filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwanta ga tsibirin na Cyprus kafin ƙarshen wannan shekarar. Idan ko ba haka ba, tattaunawa kan batun shigar Turkiyya cikin ƙungiyar EUn za ta cije, inji Merkel. Ta ƙara da cewa:-
„A nawa ganin dai, ai wajibi ne, idan mambobin ƙungiyar Hadin Kan Turai na son inganta ma’ammala da juna, su kau da duk wani shingen cinikayya tsakaninsu, abin da ya ƙunshi samun damar shige da fice a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwan kasashen ƙungiyar. A halin yanzu dai, akwai wata shawara da Finnland ta gabatar don warware wannan matsalar. Ina murna da jin cewa Turkiyya ma ta yi marhabin da wannan shawarar, kuma ina fata za mu iya shawo kan wannan mawuyaciyar matsalar, saboda ita ce sharaɗin ci gaban tattaunawa da ƙungiyar EU.“
Da yake mai da martani, Firamiyan Turkiyya Tayyip Erdogan ya bayyana cewa yarjejeniyar birnin Ankara ba Turkiyya kaɗai ta bukaci ta cika wasu sharuɗɗa ba. Tana kuma bukatar ƙungiyar EUn da ta ɗage takunkumin saniyar waren da take yi wa yankin arewacin Cyprus ɗin, inda Turkawan tsibirin ke da yankinsu. Kafin a aiwatad da wannan shirin dai, Turkiyya ba za ta canza matsayinta ba, inji Firamiya Erdogan:-
„Matsayinmu dai a halin yanzu shi ne, bai kamata ɓangare ɗaya kawai ne zai ɗau matakai kan batun Cyprus ba. Nauyi ne da ya rataya a wuyar duk ɓangarorin da wannan lamarin ya shafa. Kuma tare ya kamata su ɗau matakan neman shawo kan matsalar. Da farko dai kamata ya yi, a ɗage takunkumin cinikayya da aka sanya wa arewacin Cyprus. Kafin dai hakan ya wakana, ba za a iya sa ran ganin mun ɗau wani mataki ba. Bukatar yin hakan daga gare mu, ba nuna adalci ba ne.“
Babu shakka, ita ma ƙungiyar Haɗin Kan Turai na da nata alkawarin da ya kamata ta cika. Bisa yarjejeniyar da aka cim ma a birnin Ankara, a shekaru biyu da rabin da suka wuce dai, da kamata ya yi a ce tuni ƙungiyar EUn ta janye takunkumin da ta sanya wa arewacin Cyprus ɗin, inda Turkawa ke zaune. Wannan alkawari ne da tsohon kwamishinan kula da harkokin faɗaɗa ƙungiyar, Günther Verheugen da kansa ya yi wa Turkiyyan, don shawo kanta ta amince da shirin zaman lafiyar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsara, don cim ma haɗe tsibirin, wanda ke rabe a sassan Girkawa a kudu da na Turkawa a arewa.
A halin yanzu dai fata ake yi ta cewa, shawarar da ƙasar Finnland ta gabatar don shawo kan matsalar za ta sami karɓuwa. Shirin na bukatar ƙungiyar EUn ta sassauta takunkumin da ta sanya wa yankin arewacin Cyprus ɗin ne, sa’annan ita kuma Turkiyya a nata ɓangaren, ta buɗe tashoshin jiragen ruwanta ga jiragen Cyprus.