Ziyarar Angela Merkel a Washington
January 12, 2006Wannan dai shi ne karo na farko da shugaba mace, ta gwamnatin tarayyar Jamus, ke kai ziyara a birnin Washington, inda a nan ma ake hasashen cewa sakatariyar harkokin wajen Amirka, Condoleeza Rice da matar tsohon shugaban kasar, Hillary Clinton ne za su tsaya takarar zabe mai zuwa da za a yi na shugaban kasa.
Game da ziyarar Angela Merkel a Washington dai, jakadan Jamus a birnin, Wolfgang Ischinger, ya bayyana cewa:-
„Gwamnatin Amirka na matukar sha’awar ganin an sami kusantar juna tsakaninta da nahiyar Turai, musamman ma dai da tarayyar Jamus. A bangaren birnin Washington dai, ana daukar wannan ziyarar da muhimmanci, don inganta huldodi tsakanin Jamus da Amirka.“
An dai sami bambancin ra’ayi tsakanin kasashen biyu game da batun Iraqi. Bugu da kari kuma, shugaba Bush da shugaba Schröder ba su taba samun jituwa mai karfi sosai tsakaninsu ba. To ko yaya lamarin zai kasance yanzu, da ake da sabuwar shugaba, kuma a karo na farko mace a nan Jamus k A ganin Jackson Janes, darektan cibiyar nazarin al’adun Jamusawa na wannan zamanin da ke birnin Washington dai, akwai bangarori da yawa da kasashen biyu za su yarrje a kansu:-
„Dukkanmu na da sha’awar ganin an cim ma zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya. Kuma tare ne muke neman hanyoyin tinkarar barazanar da kasar Sin ke yi mana, a yunkurinta na zamowa fankamemiyar tattalin arzikin duniya. Muna kuma musayar ra’ayoyi a kan makomar hanyoyin samad da makamashinmu, da yin la’akari da huldodinmu da Rasha. Mu a nan Amirka da kuma nahiyar Turai na da matukar sha’awar ganin an sammi ci gaba a duniya. Mun dai fahimci cewa, babu wanda shi kadai zai iya tinkarar kalubalen da ke gabanmu. A kalla, ababan da suka wakana a shekarun baya game da yakin Iraqi na nuna mana haka.“
Gwamnatin shugaba Bush dai na kyautata zaton cewa Jamus za ta kara ba ta hadin kai wajen aiwatad da manufofinta na ketare. Ba ta dai sa ran samun amincewar Jamus wajen tura dakaru zuwa Iraqi, amma a fafutukar da ake yi na sake gina kasar, Jamus za ta iya ba da tata gudummowa, wajen kara horad da jami’an `yan sanda da kuma wasu bangarori na inganta halin rayuwar jama’ar kasar. A Washington dai, ana ganin Angela Merkel ne tamkar wata sabuwar abokiyar burmin Amirka, inji tsohon jakadan Amirka a Jamus, Richard Burt:-
„Batun da shugaba Bush da masu ba shi shawara a Washington suka fi mai da hankalinsu a kai shi ne, yadda za su shawo kan Jamus ta shiga sahun gaba a Turai da kuma gamayyar nan ta ketaren tekun Atlantika, wajen kare mata manufofinta.“
Idan dai haka ya samu, to duk wani irin sukar da Jamus za ta yi wa mahukuntan birnin Washington game da take hakkin bil’Adama ko kuma kan sansanin nan na Guantanamo Bay, ba za ta kasance wata abar damuwa gare su ba.