1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Angela Merkel zuwa Gabas ta tsakiya

January 27, 2006
https://p.dw.com/p/BvAd

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel,tana shirin kai ziyara zuwa yankin gabas ta tsakiya a mako mai zuwa.

Merkel,itace shugabar kungiyar taraiyar turai da zata fara kaiwa ziyara yankin gabas ta takiya bayan samun nasarar kungiyar Hamas .

Sai dai kuma tace ba zata gana jamian kungiyar Hamas din ba.

Kakakin gwamnatin jamus ,Ulrich Wilhelm,yace babban abokin dasawarsu shine Mahmud Abbas.

Yace akwai sharudda 4 da zasu amince ganawa da Hamas,wadanda suka hada da,Hamas din ta amince da kasancewar kasar Israila,dakatar da tashe tashen hankula,da ajiye makamanta tare da bin kaidojin yarjejeniyar zaman lafiyar yankin.

Sai dai yace,Jamus tana mai girmama sakamakon zaben,ganin cewa jamaa sun baiyana raayinsu,kuma an gudanar da zaben bisa yanci da walwala.