1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Barack Obama a gabas ta tsakiya

March 20, 2013

A ziyarar da ya ke yi a gabas ta tsakiya, shugaban Amurka ya gana da magabatan Izraela kan Iran, Siriya da taƙaddamar da Bani Yahudu ke yi da Palasɗinawa.

https://p.dw.com/p/1810v
U.S. President Barack Obama and Israel's Prime Minister Benjamin Netanyahu shake hands at a joint news conference at the Prime Minister's residence in Jerusalem, March 20, 2013. Making his first official visit to Israel, Obama pledged on Wednesday unwavering commitment to the security of the Jewish State where concern over a nuclear-armed Iran has clouded bilateral relations. REUTERS/Larry Downing (JERUSALEM - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugaban na Amurka ya ke yi a Isra'ila tun lokacin da ya fara wa'adin mulkinsa na biyu, wanda akanta shugaban ya jaddada aniyar kasarsa ta kula da tabbatar da tsaron Isra'ila

A ganawar da yayi da firaminitas Isra'ilan Benjamin Netanyahu wanda shi ne ya tarbeshi a filin saukar jiragen sama, shugaba Obama ya ce a kwai buƙatar ganin an warware rikicin da ke tsakanin Isra'ilar da Palasɗinu a cikin ruwan sanyi.

"Ba shaka ina tsammani a cikin wannan yanki a kwai alamu na samun 'yanci duk da ma irin fargabar da ake da shi na dagulewar al'amura. Ina ganin wannan ziyara tawa zata kasance wata dama ta mu tattauna batun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya tare, domin mu samar da zaman lafiya ga wannan tsarkakar kasa, muna kyautata zaton Isra'ila za ta zauna lafiya da mokwaftanta".

Tattaunawa tsakanin shugaban Amurka da na Isra'ila.

A Lokacin wa'adin mulkinsa na farko dai, Obama ya yi kokarin farfado da shirin tattaunawar zaman lafiya tsakanin Palasɗinu da Isra'ila a shekarun 2010, amma kuma shirin ya sukurkuce dan gane da gaza cimma daidaito da aka yi tsakanin sassan biyu akan matsugunan yahudawa 'yan share wuri zauna da Isra'ila ke ci-gaba da ginawa a gabar yamma da gokin jordan.

President Barack Obama meets with Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu in the Oval Office at the White House in Washington, Monday, March 5, 2012. (Foto:Pablo Martinez Monsivais/AP/dapd)
Hoto: dapd

Akan maganar kasar Iran wanda a karo da dama Isra'ila ke yi a ɓangaran ƙungiyar Palasɗinu, ana kallon wannan ziyara a matsayin wani abin da ba zai kawo wani sauyi ba kamar yadda wani jigo a kungiyar OLP wassel Abou Youssef ya baiyana.

Zanga zangar Falasɗinawa akan ziyarar ta Obama a yankin gabas ta tsakiya.

A wannan al'hamis ce aka shirya shugaba Barack Obama zai isa a Ramallah inda zai gana da Mahamud Abbas jagoran kungiyar ta OLP mai fafutukar samar da 'yancin Palasɗinu. Akan maganar ƙasar Iran wanda a karo da dama Isra'ila ke yin barazanar kai mata hari ƙasashen biyu babu wani abu sabo da suka faɗa ,haka ma bisa zance Siriya wanda watakila ake sa ran shugabannin zasu tattauna kafin shuggaban amurikan ya kammala ziyara.

Palestinians burn U.S flags during a protest against a film produced in the U.S. that they said that was insulting to Prophet Mohammad, in Khan Younis September 14, 2012. REUTERS/Ibraheem Abu Mustaf (GAZA - Tags: RELIGION CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Acan yankin Palasɗnawa dai jama'a na ci gaba da gudanar da zanga zangar adawa da ziyarar ta shugaban Amurka, wanda a cewarsu bazata sauya komai ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar