Kusan shekara daya da soma mamayar Ukraine
February 20, 2023Shugaban Amirka Joe Biden zai kai ziyarar aikin kasar Poland a gobe talata, inda zai gabatar da jawabi a gabanin zagayowar ranar da Rasha ta kai wa Ukraine hari da nufin mamaye ta. Babban burin da Biden ya sa a gaba shi ne, taimaka wa Ukraine domin ta samu nasara a kan abokiyar gabarta.
Shugaban kasar Poland Andrzej Duda ya sanar da cewa, jawabin da takwaransa na Amirka Joe Biden zai gabatar a yammacin Talata a birnin Warsaw na da mahinmanci ga duniya baki daya. Dama dai sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya yi shagube a taron tsaro da aka yi a Munich na Jamus, inda ya ce, Biden zai yi bayani game da halin da ake ciki a Ukraine tare da ci gaba da goyon baya ga Ukraine domin ta samu nasara a kan Rasha.
Kasar Poland da sauran kasashen gabashin Turai na kungiyar tsaron NATO za su bukaci karin sansanonin sojan Amirka a kasashen, lokacin ganawa da Shugaba Joe Biden na Amirka. Amma babu tabbas kan irin amsar da za a samu daga Amirka. Duk yadda ta kasanec Amirka tana kara karfafa hulda da Poland.