Ziyarar Bush a gabas ta tsakiya a mako mai zuwa
January 5, 2008Ƙungiyar masu tsattsauran ra’ayi na Hamas dake yankin Palastiwa,tayi watsi da ziyarar da shugaban Amurka George W Bush ke shirin kaiwa yankin gabas ta tsakiya a mako mai gabatowa.Sai dai shugaban Izraela Shimon Peres ya bayyana wannan ziyarar da kasancewa wata damace na daɗa tabbatar da cimma sulhunta Izraela da yankin palasdinawan.A nashi ɓangaren shugaban na Amurka yayi fatan wannan ziyara tasa zata taimakamaka..“Bush yace zan fara yada zango a ƙasa mai tsarki,inda a nan ne zan gana da primiyan izraela Olmert da shugaba Mahmoud Abbas na yankin palastinwa.Zan karfafa ƙwarin gwiwan shugabannin biyu na cigaba da tattaunawar sulhun da suka fara a birnin Annapolis a watan Nuwamban daya gabata.Wannan babban nauyi ne,domin zai bukaci tsauraran shawarwari da tambayoyi“