1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar da shugabar jam´iyar CDU Angela Merkel ta kai kasar Turkiya. Mohammad Nasiru Awal

February 17, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlp
To yayin da shugabar ta jam´iyar CDU Angela Merkel ta yi alkawarin nuna adalci shi kuwa FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan kira yayi da a cika wannan alkawarin. Har yanzu dai ba´a kawad da bambamcin ra´ayin dake tsakanin ´yan ra´ayin mazan jiya na Jamus da Turkiya a game da daukar wannan kasa cikin kungiyar tarayyar Turai EU ba. Hasali ma abin na kara ta´azzara ne. Alal misali tun ba yau ba jam´iyar AKP ta FM Erdogan ke sha´awar ta zama memba a cikin jam´iyar Peoples Party ta Turai wato EVP, amma saboda kasancewar addinin da wannan kasa ke bi ya bambamta da na sauran wakilan jam´iyar ta Turai, sai aka ba jam´iyar ta Erdogan matsayin ´yar kallo a cikin hadaddiyar jam´iyar ta ´yan Christian democrat a Turai.

Ana iya daukar ziyarar da Merkel ta kai Turkiya da cewa ba ta haifar da da mai ido ba, amma idan aka dube ta da idanun basira, za´a ga cewar watakila ta taka wata rawa wajen samun wata kusantar juna tsakanin bangarorin biyu. An jiyo manyan mashawartan FM Erdogan, wadanda wasunsu daga Jamus suke na cewa maganar ba Turkiya wani matsayi na musamman ai sam ba ta taso ba a wannan lokaci da ake ciki.

Ita dai Turkiya tana bukatar a sanya lokacin da za´a fara tattauna batun daukar ta cikin kungiyar EU musamman don ba ta lada game da jerin sauye-sauyen inganta mulkin demukiradiyya da kasar ke yi don cika ka´idojin kungiyar EU. Bugu da kari kamata yayi shirin da Turkiya din ta nuna wajen warware rikicin tsibirin Cyprus ya taka muhimmkyar rawa wajen daga darajar wannan kasa a cikin kungiyar ta EU, musamman game da taimakon tattalin arziki. Ko shakka babu karin masu zuba jari na ketare hade da aiki tukuru zasu taimaka wajen inganta matsayin rayuwar al´umar wannan kasa daidai da takwarorinsu na Turai. Mai yiwuwa bayan haka ne za´a iya gudanar da shawarwari akan ko shin Turkiya wata babbar daula ce dake makwabtaka da Turai ko kuma a´a.

Za´a dauki shekaru masu yawan gaske kafin a kai ga wannan matsayi, to amma bai kamata a yi amfani da batun shigar da Turkiya cikin kungiyar EU wajen yakin nema zabe ko kuma kirkiro wata sabuwar baraka tsakanin Turkiya din da sauran kasashen Turai ba. A dai halin da ake ciki babu wani zabi da ya ragewa kungiyar EU face ta cika alkawuran da ta dauka, sannan kuma a wannan shekara ta ayyana ranar da zata fara tattaunawa da Turkiya game da shigar da wannan kasa cikin kungiyar.

Ko da yake mahukuntan birnin Ankara sun san cewar yanzu gwamnatin tarayyar Jamus karkashin jam´iyun SPD da Greens ke yanke hukunci a birnin Berlin kuma ta ke da fada a ji a birnin Brussels, amma dole sun hango abin da ka iya faruwa idan mulkin Jamus ya koma hannun ´yan Christian Democrat.