Ziyarar David Cameron da Nicolas Sarkozy a Libiya: gaisuwa da rokon iri
September 16, 2011Jaridun na Jamus a wannan mako, sun maida hankali musamman yadda yan siyasa na Faransa kan karbi kudaden toshiryar baki daga shugabanni yan mulkin danniya daga Afrika domin su ci gaba da goyon bayan su.
Jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba halin da ake ciki ne a Libiya, inda musamman tayi sharhi game da tserewar iyalan Gaddafi zuwa makwabciyar jamhuriyar Niger. Jaridar tace yanzu haka dai matsin lamba yana karuwa kan kasar ta Niger domin ta mika ´ya´ya da sauran iyalan Gaddafi da suka tsere kasar, cikin su har da Al-Saadi Gaddafi da ke tsare yanzu bayan da ya shiga Niger din a farkon wannan mako. Sai dai jaridar tace yayin da ake zargin gwamnatin Gaddafi da laifin kisan abokan adawa, suma yan tawayen da suka kawar dashi, basu tsira daga wannan zargi ba. Wani rahoto na kungiyar Amnesty International ya nuna cewar kan hanyar su ta kawar da mulkin Gaddafi, yan tawayen sun rika azabtar da fursunonin da suka kama, wasu sun mutu, wasu yan tawayen ma ana zargin su da laifuka irin na yaki. Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba Libiya, musamman ziyarar da Pirayim ministaan Ingila, David Cameron da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy suka kai kasar a wannan mako. Jaridar tace wadannan shugabanni biyu sun ziyarci Tripoli ne da Benghazi domin nunawa sabbin shugabannin na Libya cewar suna bukatar kasancewa kan gaba, idan har kasar ta tashi bada kwangiloli na aiyukan ci gaba ko sake ginin kasa. Wannan buri nasu ya cika, domin sun sami marhabin sha tara ta arziki a biranen da suka kaiwa ziyara, yayin da shugaban majalisar mulki ta wucin gadi, Mustafa Abdul Jalil yayi alkawarin cewar duka kasashen da suka taimaka aka kayar da gwamnatin Muammar Gaddafi, zasu sami fifiko idan aka zo rabon kwangiloli a kasar ta Libya.
A kasar Habasha da mafi yawan yankin kahon Afrika ana fama da matsalar yunwa da kuma rashin ci gaba a bangaren yancin siyasa. Jaridar Tageszeitung a nata sharhin, tace a Habasha alal misali, danne hakkin jama'a a fannin siyasa yana karuwa daidai da yadda yunwa take kara tsananta a kasar. Jaridar tace gwamnatin kama karya ta Meles Zenawi, ta hana rabon taimakon abinci a wasu wurare, ta kuma gabatar da dokokin yaki da aiyukan tarzoma masu tsanani, yadda zata rika amfani dasu kan yan adawa. Jaridar Tageszeitung tayi misali da yan kabilar Oromo da aka hana su samun agaji da ruwan sha da ko wane irin taimako duk kuwa da ganin cewar yawan su ya kai kashi 35 cikin dari na al'ummar Habasha gaba daya. Kasar da kuma yankin kahon Afrika baki daya, bisa kiyasin majalisar dinnkin duniya, a yanzu suna cikin wani hali da shine mafi muni na bala'in yunwa tsakanin shekaru 60.
A karshe, jaridar Süeddeutsche Zeitung ta duba matsayin dangantaka tsakanin shugabannin Faransa da takwarorin su masu mulkin kama karya a nahiyar Afrika. Jaridar tace shugabanni dabam dabam na Faransa sun yi shekara da shekaru suna karbar kudade masu yawa daga yan mulkin kama karya na Afirka domin su goyi bayan su su ci gaba da mulkin danniya a kasashen su. Jaridar, ta ambaci daya daga cikin yan aiken dake kaiwa shugabannin na Faransa akwatuna cike da kudi, inda tace musamman tsohon shugaban Faransa, Jacques Chirac da tsohon ministan harkokin waje, Dominique de Villepin sun karbi kyauta mai yawa daga shugabannin Senegal, Burkina Faso, Cote d'Ivoire da Congo da Gabon, kamar yadda akan ce wai kwaryar da taje, tazo, bangarorin biyu su ci ribar juna.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Yahouza Sadissou