Ziyarar Farfesa Attahiru Jega a Berlin
May 27, 2011Adaidai lokacin da ake bukukuwan rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin Nigeria, waɗanda suka yi nasara a zaɓukan da suka fuskanci takaddama a watan Afrilu, shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta na Nigeria farfesa Attahiru jega ya shawarci shugabannin da su kasance masu darajawa tsarin mulkin demokraɗiyya.
Farfesa Attahiru Jega ya ce ganin yadda tsarin mulkin Demokradiyya yake samun karɓuwa tsakanin kasashen Duniya, kamata yayi a ingantashi ya kasance da faida, domin cigaban Al'umma.
Shugaban hukumar ta INEC ya yi wannan furuci ne bayan gabatar da wata kasida kan Dimokraɗiyya da ingancin gwamnati a jami'ar Humboldt-Viadrina da ke a birnin Berlin na tarayyar Jamus.
Farfesa Jega yace inganta tsarin mulkin demokradiyya zai kare yin kaka gida akan kujerar mulki da wasu zaɓaɓɓun shugabanni ke yi.
Shugaban hukumar zaɓen Nigeria mai zaman kanta ya yi amanar cewar zaɓuɓukan watan Afrilun da suka wakana a Nigeria sun fuskanci takaddama da kura-kurai, hukumarsa tayi ginin dake bukatar cigaba da ginawa da ingantawa, tare da nazarin matsalolin domin kare sake aukuwarsu nan gaba, musamman a ɓangaren 'yan siyasa.
Acewar Jega, hakkin hukumarsa ce fitar da tsarin daya kamaci Nigeria tare da gabatarwa, sauran mahawara dangane da amincewa ko rashin amincewa da zaɓe batu ne daya shafi bangaren Shari'a.
Ya ce zaɓen watan Afrilun na Nigeriya ya taimaka wajen wanke ta a idanun ƙasashen ketare, duk da 'yan matsaloli da ya fuskanta.
Fatan da 'yan Nigeria ke yi dai shine, zaɓaɓɓun shugabannin su gudanar da ayyukan da zasu inganta rayuwarsu.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal