1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka: Fargaba kan taron Kim ad Putin

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 13, 2023

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya sha alwashin bayar da cikakkiyar gudunmawa ga takwaransa Vladimir Putin na Rasha, yayin taron da kasashen biyu da ke zaman saniyar ware suka gudanar.

https://p.dw.com/p/4WJ0h
Rasha | Vladimir Putin | Taro | Kim Jong Un | koriya ta Arewa | fargaba | Amurka
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa da takawaransa na Rasha Vladimir PutinHoto: Vladimir Smirnov, Sputnik, Kremlin Pool Photo via AP/picture alliance

Amurka ta yi gargadin taron na kasashen Koriya ta Arewa da Rasha, ka iya kai wa ga cimma yarjejeniyar mika makamai ga Moscow domin ci gaba da yakin da take da makwabciyarta Ukraine. Taron wanda ya gudana a gabashin Rashan, ya nuna yadda kasashen biyu ke da tunani iri guda da kuma aminci da juna. An dai yi amannar cewa, Vladimir Putin na Rashan zai bukaci tallafin Koriya ta Arewa kan makaman da take da su da ka iya hada wa da tsofaffin makaman da aka yi amfani da su a lokacin tsohuwar Tarayyar Soviet. Haka kuma akwai yiwuwar Shugaba Kim Jong Un ya nemi agajin Rasha wajen kaddamar da na'urar satellite, wadda ya bayyana da mai matukar amfani wajen ci gaba da yin barazanarsa ta makaman nukiliya a duniya.