Ziyarar Majalisar Dinkin Duniya a Afirka
March 3, 2017Rahotanni sun nunar da cewa miliyoyin mutane ne ke fuskantar tsananin barazanar yunwa sakamakon wannan rikici da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al'umma tare da tilasta wasu masu tarin yawa zuwa gudun hijira, a wasu kasashe da ke yankin Tafkin Chadi. Da yake jawabi ga manema labarai jakadan Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniyar, Matthew Rycroft ya nunar da cewa sun fara ziyarar ne domin nuna wa al'ummar da ke cikin halin tasku cewa ba a manta da su ba. Majalisar Dinkin Duniya dai ta kaddamar da asusun tallafi na dalar Amirka biliyan hudu ga yankunan da rikicin ya shafa a Najeriya, kana ta kaddamar da makamancin wannan tallafi ga Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Yemen da suma ke fama da yakin wanda ya haddasa tsananin barazana ta yunwa a cikinsu.