Wakilan Musulmai da na Yahudawa a Auschwitz
January 27, 2020Tattakin da aka samu tsakanin shugabannin Yahudawa na Amirka gami da shugabannin kungiyar Musulmai na duniya da wata kungiya mai zaman kanta, a sansanin nan na gwale-gwale na Auschwitz da ke kasar Poland, inda aikata kisan kare dangi musamman a kan Yahudawa ya kasance daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankali yayin bikin cika shekaru 75 da kawo karshen sansanin na 'yan Nazi lokacin yakin duniya na biyu.
Yana da matukar wuya a ji magana da harshen Larabci a wajen tunawa da mutanen da suka mutu a sansanin gwale-gwalen na Auschwitz da ke zama mafi girma da ke Birkenau a kasar Poland, inda Larabawa kalilan suka kai ziyara daga cikin fiye da mutane miliyan biyu da suka kai ziyara a shekarar da ta gabata. Sheikh Mohammed Al-Issa ba kawai ya kai ziyara ba ne, amma tare da shugabannin Yahudawa, wadda suka tsara da shugabannin Yahudawa na Amirka.
Al-Issa shi ne sakataren janar na wata kungiyar Musulman Duniya mai zaman kanta da ke kasar Saudiyya ya bayyana abin da ya faru a sansanin a matsayin laifi ga dan Adam, kuma ya yi addu'o'i lokacin da ya fuskanci alkibla kamar yadda wakilin DW ya ruwaito a cikin wani bidiyon da ya hada.
Kimanin mutane rabin miliyan sun kalli wannan faifayen bidiyo da aka yada kan ziyarar a shafin sada zumunta na Twitter, wanda 'yan jarida na Isra'ila suka saka. Haka ya nuna Yahudawa da Larabawa za su iya hada kai ziyarar idan aka yi kisan kare dangin.
Albarkacin cika shekaru 75 da kwace sansanin gwale-gwalen daga hannun dakarun Nazi na shugaban gwamnatin Jamus na wancan lokacin Adolf Hitler, shugabannin na Musulmai da Yahudawa sun kai ziyarar gami da wurin bauta na Yahudawa, kuma ga abin da daya daga cikin shugabannin na Musulmai, Sheikh Mohammed Al-Issa ke cewa.
"Na zo da wakilai daga kasashen Musulmai domin shaida wa kowa mun yi kakkausar suka kan laifin da aka aikata da ya jijjiga dan Adam. Mun ga wajen da aka yi amfani da gas mai guba domin kona mutane. Fiye da Yahudawa miliyan daya aka kashe saboda kawai su Yahudawa ne. Mata, yara matasa wadanda ba su san hawa ba bare sauka 'yan Nazi sun halaka, wadanda suke da akida da nuna tsana da share wata al'uma daga doron kasa."
Sannan Al-Issa ya kara da cewa duk wanda yake goyon baya ko nuna tausayi ga 'yan Nazi ko kuma neman hanyar wanke ta'addanci da suka yi, ya kamata a soke lamirin abin da yake yi. Shi dai Al-Issa ya kasance tsohon ministan shari'a na Saudiyya.
Daya daga cikin shugabannin Yahudawa a Birtaniya, David Rosen ya tuno da tarihi a wajen bautar Yahudawa da ke birnin Warsaw na kasar Poland kan abin da marigayi Paparoma John Paul na biyu ya fada game da muhimmancin addinai uku na Yahudawa da Musulmai gami da Kiristoci.
"A matsayin zuri'ar Annabi Ibrahim za mu kasance abin alfahari da dan Adam. Kafin haka ya kasance sai mun zama abin alfahari tsakaninmu. Na yi imani a matsayin dangantaka tsakanin Yadudawa da Musulmai hada kan ya zama hanyar zama abin alfahari da juna. Allah Ya ba mu nasara da juriya."
Kasar Saudiyya ke kan gaba wajen samar da kudin tafiyar da wannan kungiyar Musulmai mai zaman kanta da ta kunshi Musulmai daga sassan duniya dabam-dabam.