1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Merkel a ƙasar Rasha

April 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0T

Shugabar gwamnatin Jamus Angela da takwaranta na ƙasar Rasha Vladimir Putin, sun fara tattaunawa ta yini biyu a game da batutuwa da suka shafi harkoki na diplomasiya. A zagayen farko na ganawar ta su wadda ta gudana a birnin Tomsk dake yammacin Siberia, shugabannin biyu sun jaddada ƙudirin ƙarfafa muámala ta cudanni in cude ka, tare da fahimtar juna a tsakanin su. Tattaunawar ta kuma taɓo batun samun daidaito a harkar samar da makamashi. A halin da ake ciki kamfanin gas na ƙasar Rasha Gasprom shi ne yake samar da kashi ɗaya bisa uku na makamashin iskar gas ga nahiyar turai. A yau alhamis ake sa ran shugabanin biyu za su sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta tattalin arziki a tsakanin ƙasashen na Jamus da kuma Rasha.