Ziyarar Merkel a Amirka
June 7, 2011Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta isa birnin Washington, fadar gwamnatin Amirka domin ziyarar aiki ta yini biyu, wadda a lokacin ne kuma za ta karɓi lambar girmamawa ta shugaban ƙasa akan 'yanci. Za'a dai gudanar da shagalin miƙa mata kyautar ce yayin cin abincin dare a fadar shugaban Amirka ta White House a wannan Talatar.
A halin da ake ciki kuma, Merkel, tare da wasu ministoci biyar na gwamnatin Jamus dake rufa mata baya a ziyara zuwa Washington ɗin, za su gana tare da shugaba Barack Obama da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin Amirka, inda za su tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi halin da ake ciki a ƙasashen Larabawa da kuma rikicin da takardar kuɗin Euro ya faɗa ciki, kana da batun manufar da ta shafi makamashi.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu