Ziyarar Merkel a Turkiya
March 29, 2010Duk da tattaunawa mai zurfi da suka yi a birnin Ankara, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan, ba a samu kusantar juna tsakaninsu ba a kan muhimman batutuwa da suka haɗa da shigar da matasa Turkawa cikin harkokin yau da kullum a Jamus da batun shirin nukiliyar Iran da kuma ɗaukar Turkiya a cikin Ƙungiyar Tarayyar Turai EU. Merkel ta ƙarfafa cewa dole ne matasan Turkawa su saje cikin Jamusawa domin su samu dama daidai wa daida da sauran ´yan ƙasa a makarantu da kuma wuraren sana´a.
Merkel ta bayyana taƙaddamar da ake yi game da tsibirin Cyprus a matsayin babbar matsala ga samun kusantar juna tsakanin Turkiya da ƙungiyar EU. Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kuma ƙara jaddada cewa Jamus na martaba tattaunawar ɗaukar Turkiya ɗin cikin EU da aka fara a shekara ta 2005 kuma tana girmama ƙa´idojin aiki da yarjejeniyoyin da aka ƙulla.
"Mun amince kan ci-gaba da tattauna batun shigar da Turkiya cikin EU. A gani na muhimmin batu na warware matsalar shi ne yarjejeniyar birnin Ankara. To sai dai yanzu muna cikin wani hali ne inda ba a tantance batun tsibirin Cyprus ba. Duk da saɓanin da ke tsakaninmu dangane da bawa Turkiya cikakken wakilci, za mu ci-gaba da bin wannan hanya, kuma na yi imani za mu yi amfani da lokacin da ya rage mana don tattauna batun Cyprus domin samun maslaha."
A cikin yarjejeniyar birnin Ankara dai wadda aka cimma a shekarar 2005 an faɗaɗa ayyukan jami´an kwasta tsakanin EU da Turkiya da kuma jerin sunayen sabbbin membobin EU ciki har da Cyprus. To sai dai saɓanin dokokin EU har yanzu Turkiya ta ƙi buɗe filayen jiragen samanta da tashoshin jiragen ruwanta ga Cyprus.
A game da taƙaddamar nan ta buɗe wata makarantar sakandaren Turkawa a Jamus kuwa Merkel ta ɗan nuna kusanci ga Firaministan Turkiya Tayyip Erdogan. Merkel na mai ra´ayin cewa idan Jamus ta na da makarantun Jamusawa a wasu ƙasashen ciki kuwa har da Turkiya to babu laifi idan Turkiya ta buɗe makaranta a Jamus.
A ƙarshen mako dai Erdogan ya soki Merkel da kakkausan harshe bayan da shugabar gwamnatin ta nuna adawa da buɗe makarantar Turkawan a Jamus. Jami´ar dake kula da batun zamantakewa a Jamus Maria Böhmer wadda ke yiwa Merkel rakiya a wannan ziyara, ita ma ta nuna adawa da buɗe makarantar da cewa mayar da hannu agogo baya bisa manufar sajewar baƙi cikin Jamus.
"Idan ana maganar kyatatuwar ilimi a nan Jamus to an san ƙoƙarin da muke yi bisa wannan manufa. Mun nunar a fili cewa duk mai son samun ci-gaba mai ma´ana a Jamus ko zama na dindindin a ƙasar to dole ne ya naƙalci harshen Jamusanci."
A wannan Talata rana ta biyu kuma ta ƙarshe ta wannan ziyara, Merkel za ta ziyarci wani cocin Evangelika da kuma makarantun Jamusawa a birnin Istanbul.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas